Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkaida Ta Fitar Da Hotunan Wasu Mutane Da Ta Kame


Reshen al-Qaida na Afrikata Arewa ya sako hotunan mutanen da yace hudu ne daga cikin turawan daya cafke a Junhuriyar Nijer.

Cibiyar IntelCenter dake Amurka, wace ta gwanance wajen nazarin irin wadanan sakkonin, ta tabattarda cewa lalle al-Qaida ta nuno wadanan hotunan da suka hada da na wasu mutane biyu mace da namiji 'yan kasar Switzerland da wata mace Bajamusa da kuma wani baturen Ingila guda daya.

Sako wadanan hotunan ya biyo bayan sanarwar da wani kakakin kungiyar ta al-Qaida mai suna Salah Abu Mohammed ya bada ne, na cewa sun kuma sace wasu jami'an diplomasiya guda biyu na kasar Canada hade da turawa hudu masu yawon shakatawa a can cikin Afrika ta Yamma.

Kakakin yace al-Qaida na da cikakken 'yancin sarrafa wadanan turawan yadda taga dama ta hanyar aiwatarda tsarin shari'ar islama a kansu, sannan ya karasa da cewa sai a wata rana ta nan gaba zasu baiyana sharuddan sakinsu.

XS
SM
MD
LG