Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Sayi Jarin Daga Wasu Bankuna KAsarta


Hannayen jari a kasuwannin ƙasashen Asiya da kuma turai sun sake cirawa yau, yayin da ’yan kasuwa suke dakon cikakken bayanin shirin gwamnatin Amurka na sayen hannayen jari a Bankuna na kimanin dala miliyan dubu ɗari biyu da hamsin,daga Bankuna masu zaman kansu.

Shugaba George Bush ya sanar da cewa gwamnati zata sayi hannayen jari a Bankunan domin samar da kuɗi kai tsaye, a yunƙurin gwamnatin na baya bayan nan, na sake maido da martabar bankunan. Ceto fannonin kasuwancin da gwamnati zata yi zai taimaka wajen samar da kuɗi ga bankuna yadda zasu ci gaba da bada rance.

Jami’ai suka ce shirin zai haɗa da tsayawa bankuna na ɗan takaitaccen lokaci domin su iya neman bashi tsakanin junansu, wani abinda yake da muhimmanci a tsarin bada bashin kuɗi na ƙasar Amurka. Wannan duka yana cikin shirin ceto fannonin kasuwanci na dala miliyan dubu ɗari bakwai da Majalisa ta amince da shi farkon watan nan.

Gwamnatoci a duk faɗin Duniya sun yunƙura wajen ceto bankunansu domin gudun kada ƙasashen Duniya su fuskanci koma bayan tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG