Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Afghanistan Na Tattauna Matsalar Tsaro


Shugaba Karzai ya baiyana karara cewa har yanzu da sauran rina a kaba, a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afghanisatan. Yace “Hakika yanayin tsaro a Afghanistan ya tabarbare a ‘yan shekarun nan da suka shude. Wannan ba ko tantama.

A wata hira da gidan talbijin na CNN yayi dashi kafin tasowarsa daga Kabul zuwa birnin Washington, Shugaban na Afghanistan ya lissafa abubuwan da yake burin tattaunawa da Shugaba Bush.

Yace ganawar tasu ta kwana biyu a fadar shakatawa ta Camp David, zata tabo batutuwan yaki da ta’addanci, hana fataucin miyagun kwayoyi, karfafa rundunar sojin Afghanistan, da kuma yadda za a takaita kashe kashen farar hula a tashe tashen hankulan da ake ta faman yi a kasar.

Jami’an gwamnatin ta Afghanistan, sun sha kokawa da yadda dakarun kawancen kasashe ke ta karkashe mata da kananan yara, a farautar da suka ce suna yi, ta ‘yan Alka'ida da birbishin ‘yan kungiyar Taliban. Shugaba Karzai yace idan dai ba wani mataki aka dauka wajen hana wannnan ta’asas ba, to babu shakka kuwa kwarjini da kimar dakarun zata kara zubewa a idanun jama’a.

Yace “Wajibi ne muyi wani abu, wani abu ta fuskar daukar matakan rage yawan kisan farar hula. Yace “Suna goyon bayan yakin da ake yi da ta’addanci, kuma tilas ne a irin wannan hali, ka kare wanda ke goyon bayanka.”

Da aka tambayeshi ko me zai ce game da farautar Usama Bin Laden da ake yi, sai Karzai yace ai Amurka da kawayenta basu ma kai kusa da inda suka kai ba a’yan shekarun nan. Ya ka kara da cewa shi ya ma tabbatar Bil Laden baya cikin Afghanistan a halin yanzu. Saidai yaki yarda ya fadi inda yake zaton za a same shi.

XS
SM
MD
LG