Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Sabuwar Hanyar Yakar Maleriya


Wani kifi da aka sanshi da sunan Tilafia, ko karfashe a kasar Hausa, yana cinye ‘ya’yan sauro, idan suka kyankyashe a cikin ruwa. Amma in banda yanzu da masanan suka binciko, ba a taba auna yadda yake hana yaduwar saurayen da suke haddasa cutar maleriya ba.

Masu binciken sun zuba wannan kifi na karfashew a wadansu kududdufai, a bakin gabar kogin Victoria, wani wuri da dimbin sauraye masu haddasa maleriya ke rayuwa, kuma su hayayyafa.

Bayan kusan shekara daya, sai suka ga yawan sauron dake rayuwa a wajen, ya ragu da misalin kashi 94 bisa dari.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Naorobi, yace wannan bincike zai bayar da karin damar ceton rayukan mutane da dama a Kanya, inda ciwon maleriya yafi ko wacce cuta kashe jama’a.

Maleriya tana kashe fiye da mutum Miliyan daya a ko wacce shekara, a kasashen bakaken fatar Africa, kuma yawancinsu yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar.

XS
SM
MD
LG