Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rataye Taha Yasin, Tsohon Mataimakin Shugaba Saddam Hussain


Da misalin karfe uku da minti biyar na safe agogon Bgadaza, aka rataye Taha Ramadan Yasin a wata marataya dake sansanin soja da yan sanda a arewacin Bagdaza, wanda a da shine sakatariyar yan sandan ciki na Saddam Hussein.

Cikin watan Nuwamba aka yankewa Ramadan hukuncin kisa, saboda tilastawa mutane su bar muahllansu, cin zarafin bil’adama, da kuma rawr da ya taka a kisan mutane 148 yan mashabin shi’a maza da kananan yara a garin Dujail, bayan wani yunkurin hambare saddam Hussein da bai sami nasaraba.

Da farko an yankewa Ramadan, mai shekaru kimanin 70 a duniya hukuncin daurin rai da rai, amma sai kotun daukaka kara tace wannan hukuncin anyi masa sassauci ainun, ta mai dashi hukuncin kisa.

A lokacin da aka yanke masa hukuncin, Ramdan yace bashi da laifi, ya kuma la’anci wadanda yace basuyi masa adalci ba. Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa, da kuma shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya duk sun soki hukuncin kisan saboda babu isassun shaidu da suka tabbatar da hannunsa a kashe kashen na Dujail.

Shi dai Taha Yassin Ramadan shine mutum na uku cikin mukarraban saddam Hussein da ka kashe saboda laifuffukan da akayi a Dujail. Tsohon shugaban kasar an kasheshine ranar 30 ga watan Disamba.

Wani Jami’in Iraqi yace ratayar bata zo da wata matsala ba. Idan za’a iya tunawa, ratayar saddam Hussein ta jawo suka a duniya baki daya, bayan da wani faifnn video ya nuna ana zolayarsa, dab da a ratayeshi. Haka ratayar tsohon shugaban yan sandan cikin Saddam Hussein, Barzan Ibrahim al-Tikriti, shima ya sha suka domin ratayar ta raba kansa da gangar jiki.

XS
SM
MD
LG