An shiga wani halin rashin tabbas dangane da wanda zai zama Firayin Ministan Isra'ila na gaba, saboda kowa daga cikin manyan jam'iyyun kasar biyu, suna da'awar nasara a babban zaben kasar.
Bayan an kammala kidaya kashi 99 bisa dari na kuri'un da aka kada, Jam'iyya mai mulki ta Kadima, wadda ke karkashin jagorancin Tzipi Livni, ta sha gaban jam'iyyar 'yan mazan jiya ta Benjamin Netanyanhu da kujera daya jal a Majalisa.
Masu sharhi kan al'amuran siyasar kasar sunce ko an kammala kirga ragowar kuri'un, babu daya daga cikin manyan jam'iyyun da zata sami rinjayen da ake bukata, domin kafa gwamnati, gashi kuma Netanyanhu ya ki ya mika wuya, bare ya amince a kafa gwamnatin hadin guiwa.
Sudai
masu kada kuri'a sun ce tsaro shine babban al'amarin dake gabansu, abin da yasa
suka kada wa 'yan mazan jiya kuri'u masu yawa, kamar yadda Avigdor Liberman,
shugaban wata karamar jam'iyya ta Yisrael Beiteinu ya fada.
Liebaerman
yace tilas ne a bada fifiko ga yaki da ta'addanci, kuma basu yarda da wata
tattaunawa cikin sulhu ba, ko ta kai tsaye, ko ta bayan fage.Liberman
yana ma da ra'ayin a ware dukkan 'yan kasar ta Isra'ila masu jinin larabawa, a
maida su karkashin mulkin Falsadinawa.
Wani
Farfesan kimiyyar siyasa a Jami'ar Hebrew, Abraham Diskin yace mai yiwuwa
Netanyanhu ya dare kujerar ta Firayin Minista, duk da cewa yana bayan Livni da
kujera daya, saboda kananan jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya sun fi yawan
kujeru a majalisar. Saidai yace lallai ne Netanyanhu ya bi sannu wajen zaben
wadanda zai kafa gwamnati dasu.
Yace 'Yan
mazan jiyan da yake hange, ba lallai su zama masu ra'ayi irin nasa ba, kuma
jam'iyyu shida ne masu alkibla bambancin alkibla kan muhimman al'amuran da suka shafi Isra'iala.