Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sayar Da Wani Tsohon Makullin Ka'aba Dollar Miliyan Goma Sha Takwas


Anyi gwanjon wani tsohon makullin Dakin Ka’aba Mai Tsarki, wanda aka yi amfani da shi tun a karni na 12, inda aka sayar da shi fiye da dollar miliyan guma sha takwas.

A birnin London aka sayar da makullin, wanda aka yi amfani da shi tun zamanin mulkin Abbassiyya, kuma ba a ma san wanda ya sayi makullin ba.

Darajar makullin, wanda a da, da shi ake bude kofar dakin mafi tsarki a duniyar musulmi dake birnin Makka, ta minka kimar da aka yi masa har sau goma sha takwas.

Haka kuma a wani gwanjon, an sayar da wani tsohon takobin zinare, mallakar wani sarkin Indiya, Shah Jahan kan dollar miliyan uku. Shi dai Sarki Shah Jahan, shine ya gina gidan nan mai tarihi na Taj Mahal.

XS
SM
MD
LG