Daraktan
Hukumar Leken Asiri ta Amurka, wato CIA, yace da alamu wadansu zarata sun karbe
ragamar tafiyar da al’amuran kungiyar Alkaida daga hannun Shugabansu Osama Bin
Laden, shi kuwa sun kyle shi ya ji da tsaron lafiyarsa kawai.
Michael
Hayden ya fada a wani jawabi da ya gabatar a nan birnin Washington jiya
Alhamis, cewa har yanzu farautar Bin Laden tana daga cikin muhimman al’amuran
da suka sa a gaba.
Hayden yace
watakil Bin Laden yana nan a labe a wani sako, tsakanin kan iyakokin
Afghanistan da Pakistan.
Shugaban na
CIA ya kuma ce kama Bin Laden, ko ma kashe shi kwata kwata, zai karya zuciyar
magoya bayan da almajiran sa.
Hayden yace
har yanzu, Alkaida ita ce kungiya mafi barazana ga tsaron Amurka, kuma idan har
aka sami wani hari kan Amurka, to ko shakka babu za a sami annun alkaida a
ciki.
Yace Alkaida tana kuma yada manufofi, tare da samun karin tagomashi a Afirka da Gabas ta Tsakiya.