Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jiaran Sakamakon Zabe A Ghana


Sakamakon farko daga zaben shugaban kasa a Ghana ya nuna cewa har yanzu babu fitacce a tsakanin dan takarar jam’iyya mai mulki da na babbar jam’iyyar hamayya.

Sakamakon da kafofin yada labarai na Ghana suka bayyana a yau litinin ya nuna cewa John Atta Mills na jam’iyyar hamayya ta NDC yana gaba da kimanin kashi 50 cikin 100, ya ba Nana Akufo-Addo na jam’iyyar NPP mai mulki rata amma ’yar kadan.

Mutanen biyu su na takarar neman maye gurbin shugaba John Kuffour, wanda zai sauka a bayan da ya kammala wa’adi biyu na shekaru hurhudu da tsarin mulki ya kyale shi. Nan da jibi laraba ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben daga hannun hukuma.

Masu fashin baki da dama sun ce tana yiwuwa sai an gudanar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani a tsakanin manyan ’yan takarar biyu. Haka kuma, masu rajistar jefa kuri’a miliyan goma sha biyu na Ghana sun zabi wakilan majalisar dokoki a zaben na jiya lahadi. ’Yan kallo sun ce an gudanar da wannan zabe cikin lumana.

XS
SM
MD
LG