Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aski Ya Fara Zuwa gaban Goshi A Siyasar Amurka


‘Yan takarar Shugabancin Amurka, John McCain na Jam’iyyra Republican da Barack Obama na Democrat, sunci gaba da zargin juna, kan manufofinsu na tattalin arziki, a yayin da ya rage kasa da makonni biyu a gudanar da zabe.

Sanata Obama wanda ke kan gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a, ya gudanar da yakinsa na neman zabe a jihar Indiana, jihar da rabon da ta zabi dan democrat tun shekarar 1964.

Ya zargi McCain da bada fifiko ga kyautatawa kamfanoni fiye da ma’aikata, a manufofinsa na tattalin arziki.

Juma’ar nan Obama zai katse yakin neman zaben nasa, domin ya ziyarci kakarsa mai shekaru 85, wadda ke fama da jiki a Hawaii.

Shi kuwa McCain yana can jihar Florida yana nasa yakin neman zaben, inda ya shirya wani zagaye a cikin motar safa da ya rada wa suna “Joe the plumber.”

Shima ya soki lamirin manufar tattalin arzikin Obama, wadda yace ta dauko tsarin ‘yan gurguzu, na kwata daga hannun masu shi, a raba wa talakawa.

Masu sharhi a kan al’amuran siyasar Amurka dai sun yi ittifakin cewa Obama yana baiwa McCain rata a kuriar jin ra’ayin jama’a.

XS
SM
MD
LG