Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bhutto Ta Bukaci Ayi Cikakken Bincike Kan Harin Da Aka Kai Mata


Masu bincike a Pakistan yanzu suna kyautata zaton cewa ‘yan kunar bakin wake biyu ne mai makon mutum guda suka kai harin kan jerin gwanon motocin tariyar tsohuwar PM kasar Benazir Bhutto.

Masu nbincike a Karaci sunce tuni suka gano kan mutum na biyu da ake zargi da kai harin,kuma suna kokarin sake hada fiskarsa domin gane ko wanene.

Haka kuma yau din, Malama Bhutto ta ziyarci makwancin wadda ya kafa kasar Pakistan Mhammed Ali Jinnah,kuma ta sake nanata kiranta na kafa kwamiti mai zaman kansa na kasa da kasa domin binciken harin.

Ahalin yanzu kuma,hukumomin kasar suna shawarar hana jerin gwanon siyasa bayan harin bam da aka auna kan tsohuwar PM kasar Benazir Bhutto Alhamsi da ta shige har ya kashe kusan mutane 140.

Mukaddashin Ministan yada labarai Tareeq Azim ya gayawa manema labarai yau litinin cewa, Gwamnati tana son soke manyan tarukan siyasa. Yace ana iya yin kananan tarurrukan a wani kayyadajjen wuri karkashin tsauraran matakan tsaro. Musa lura da al’amura sunce kayyade yakin neman zabe zaiyi rauni ga sahihancin zabe mai gabatowa.

XS
SM
MD
LG