Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Cikar Shekaru 90 Da Kammala Yakin Duniya Na Daya


Ana bukukuwa a duk faɗin Amurka da ƙasashen Turai da kuma Australia yau Talata, domin tunawa da cika shekaru casa’in da kawo ƙarshen yaƙin Duniya na ɗaya, babban yaƙi na farko da aka yi a cikin ƙarni ashirin.

A birnin London, tsofaffin sojoji guda uku da suka rage da rai, cikin waɗanda suka yi yaƙin Duniya na ɗayan, waɗanda dukansu suka ba shekaru 100 baya, sun jagoranci bukin tunawa da ainihin lokacin da aka sa hannu a yarjejeniyar janye musayar wutar, a sa’a ta goma sha ɗaya ranar goma sha ɗaya ga wata na goma sha ɗaya, shekara ta dubu da ɗari tara da goma sha takwas.

A wani lokaci yau, mataimakin shugaban ƙasa Dick Cheney, zai yi jawabi a wajen bukin jera furanni da za a yi a makabartar ƙasa dake Arlington,dake fitar birnin Washington. Amurka tana wannan bukin tare da karamta miliyoyin Amurkawa waɗanda suka yi yaƙi a dukan yaƙe yaƙen da Amurka ta yi a har zuwa wannan rana.

XS
SM
MD
LG