Shugaba Bush na Amurka ya sake jaddada cewar Gwamnatinsa zata ci gaba da ɗaukan matakan gyara tsarin tattalin azrikin Amurka domin kawo ƙarshen rikicin da aka samu a kasuwannin hada-hadar hannayen jari.
Shugaban na Amurka yace samun cikaken haɗin kan da aka yi daga shugabannin Turai ya taimaka ƙwarai dagaske, kuma a gobe Asabar In sha-allah za’a kammala nazartar dukkan shawarwarin da aka bayar tare da shugaba Sarkozy na Faransa.
Wata sanarwar da ta fito daga ma‘aikatar cinikayyar Amurka a yau na cewar an sami raguwar gine-ginen sabbin gidaje sun yi ƙasa da kashi goma sha bakwai daga cikin ɗari, mafi ƙanƙanta ke nan a watan satumban da ya gabata.