Shugaba George W. Bush yayi
ban kwana da fadar White House a matsayinsa na Shugaban Amurka.
Mr Bush da uwargidansa Laura
sun halarci wajen rantsar da Shugaba Barack Obama, wanda ya gaje shi.
Tun da safe saida Mr. Bush da
uwargida Laura, suka karbi Shugaba Barack Obama da uwargida Michelle a fadar
White House, inda suka yi karin kumallo tare, daga inda suka wuce harabar
Majalisar Dokoki kai tsaye domin bikin kaddamarwar.
Mr. Bush ya bar ofis da mafi
karancin tagomashi da wani Shugaban Kasa mai barin gado ya taba fuskanta a
tarihin siyasar Amurka.
Bayan kammala bukukuwan
rantsuwar, iyalin na Bush sun shiga jirgi mai saukar ungulu, zuwa filin jiragen
saman Dakarun saman Amurka na Andrews, dake nan bayan garin Washington, inda za
a yi masa bukukuwan ban kwanan kafin ya tashi zuwa Texas.
Kafin ya bar ofis, saida
tsohon Shugaba Bush ya barwa Shugaba Obama wata takarda kan teburinsa dake ofishin
shugaban kasa. Kakakin Shugaba Bush Dana Perino tace Mr. Bush ya bar takardar a
cikin aljihun teburin a jiya da dare. Saidai bata yi bayanin abin da takardar
ta kunsa ba.
Mr. Bush zai halarci wani bikin yi masa maraba da dawowa gida a kauyensu na Midland, Jihar Texas, kafin ya zarce zuwa gidan gonarsa dake Crowford. Daga karshe dai Bush da uwargidansa zasu koma Dallas, bayan kammala 'yan gyare-gyare.