Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Da Yahudawa Sunci Gaba Da Tattauna Sulhu


Jami‘an Isra’ila da na Falasdinawa sun sake wani zagayen zaman tattaunawar neman zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya, amma anji jami’an na kukan cewa babu wani ci gaban azo a gani da suka cimma, a zaman tattaunawr tasu jiya litinin.

Jami‘an Falasdinawa sun ce ba zasu saurari wani batun tattaunawa ba sai Isra’ila ta fara amincewa da zata tsaida ginin gidajen ’yan kakagidan da take yi yanzu a yankin Birnin Kudus.

Babban jami’in Falasdinu Saeb Erekat yace zaman na jiya litinin an kusa murza gashin baki. Su kuma jami‘an Isra’ila sun maida martani da cewa wajibi ne shugabannin Falasdinawa su dauki matakan hana ’yan tsagera harba rokoki zuwa cikin Isra’ila da Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.

Wani lokaci a wannan makon ne shugaban Falasdinu Mahmud Abbas da Friministan Isra’ila Ehud Olmert zasu sake zama domin tattaunawa.

XS
SM
MD
LG