Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

G-8 Sunyi Barazanar Tsaurara Matakai A Kan Farisa


Ministocin Harkokin Wajen Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Rasha da Amurka sun bayar da wata sanarawa da yammacin Laraba, inda suke nusar da kasar ta Iran, kan hadarin dake tattare da biris din da take yiwa wa’adin Majalisr Dinkin Duniya na ta dakatar da aikinta na Nukiliya.

Sun baiyana damuwarsu da abin da binciken baya-bayannan na Hukumar Kula Da Al’amuran makamashin Atom, ya gano cewa Iran ta ma fadada aiyukanta na Nukiliya. Tun da fari saida mai wakiltar Iran a kan tattaunawar da ake yi a kan Nukiliyar tata, Ali Larijani yace dakatar da aikin inganta makamashin Uranium din ba zai taimaka wajen warware matsalar da Iran take da ita da manyan kasashen yammacin duniya ba.

Alhamis dinnan zai gana da mai bada shawara kan al’amuran hulda da kasashen waje, na Kungiyar taraiyar Africa Javier Solana, a kan wannan batu na Nukiliya.

Tehran dai taci gaba da yin kemaimai ga kasashen duniya dake ta iza wutar sai ta dakatar da aikinta na inganta makamashin uranium, saboda zargin da suke yi cewa zata iya anfani da wannan dama ta kera makaman nukiliya.

A halin yanzu dai iran tana karkashin wani kwarya kwaryan takunkumi saboda kin yarda ta dakatar da aikinta na inganta makamashin uranium.

Iran dai taci gaba da musanta zargin da Amurka da saura kasashe keyi, na cewar tana kokarin kera makaman Nukilkiya, inda tace ita shirinta na zaman lafiya ne.

XS
SM
MD
LG