Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tana Shirin Tallafawa 'Yan Gudun Hijira a Kwango.


Cibiyar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniy tace a shirye take ta sakewa a ƙalla ’yan gudun hijira dubu talatin matsuguni,waɗanda suka ƙauracewa gidajensu daga gabashin Dimokuraɗiyar Congo.

A cikin jawabin da ta gabatar yau, ƙungiyar tace farin kayan da suka ƙauracewa matsugunansu suna sansanonin dake kewayen Kibati a yankin arewacin Goma babban birnin lardin Kivu. Sansanonin dake kurkusa da yankin da ’yan tawaye ke musayar wuta da dakarun gwamnati da kuma mayaƙan sa kai dake goyon bayan gwamnati.

Kakakin yace ’yan gudun hijira suna zama cikin fargabar kai masu hari da kuma wawashe ƙaddarorinsu da sojoji ke yi a lokacin rikicin. Majalisar Ɗinkin Duniy ta bayyana cewa za a fara fitar da marasa lafiya da tsofaffi da kuma ƙanannan yara zuwa waɗansu sansanonin dake yammacin Goma.

XS
SM
MD
LG