Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Bom A Lebanon Ya Sosa Ran Rice


Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tace harin yayi sanadiyyar mutuwar mutum hudu, dukkansu babu ba’amurke, ta kuma lalata wannan mota mau sulke ta Ofishin Jakadancin.

Sakatariyar Harkokin Waje, Condoleezza Rice tace duk ma wadanda ya kai wannan hari, su sani cewa ba zasu iya musgunawa Amurka ba. Tace Hakika wannan ba zai kashe guiwar Amurka ba, a kokarin ta na taimakawa kasar Lebanon, da tabbatar da dorewar dimokradiyyar kasar, su kuma taimaka wajen girgije tagomashin kasashen waje a harkokin su na cikin gida.

Rice tayi magana a birnin Riyadh, inda Shugaba Bush ya shafe kwanaki biyu yana tattaunawa da hukumomin Saudi Arabiya. Sakatariya Rice ta shaidawa manema labarai cewa Labanon na daya daga cikin batutuwan da aka tattauna, musamman ma shirin kasashen larabawa na warware rikicin dake addabar kasar, za zaben sabon Shugaban Kasa.

Tace Manufar Amurka ta dace da shirin kasashen larabawa, musamman ma dangane da batun cewa ya kamata a karfafa guiwar mutanen Lebanon, a kuma kyale su su zabi Shugaban da ransu ke so. Ya kamata a bar su suje Majalisar Kasa, su zabi Shugaban da sukai amannar zai aiwatar da muradinsu.

Tun a watan Nuwamban da ya gabata Wa’adin tsohon Shugaba Emille Lahoud, wanda ke dasawa da kasar Sham, ko Syria, ya kare, amma takaddama tsakanin ‘yan Majalisa masu goyon bayan muradun kasashen turai, da masu goyon bayan Hizbullah, ta hana a zabi sabon shugaba.

XS
SM
MD
LG