Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India da Pakistan, Sun Bude Kasuwanni A Yankunan Kashmir dake Karkashin Ikon Ko Wani Bangare


Ƙasashen India da Pakistan sun buɗe wata hanyar cinikayya karo na farko cikin kimanin shekaru sittin a kan iyakar yankin Kashmir da aka raba tsakanin ƙasashen biyu da ake rikici a kai.

Jama’a sun yi ta kuwar nuna goyon baya yayin da kwambar manyan motoci guda 13 shaƙe da kayan marmari, zuma, da waɗansu kayayyakin masarufi, suka ƙetara zuwa Kashmir da ke ƙarƙashin ƙasar Pakistan yau, daga ɓangaren India. Manyan motoci goma sha huɗu kuma daga ɓangaren Pakistan zasu tashi zuwa yankin India nan gaba. Sai dai an ƙayyade cewa manyan motoci huɗu kawai daga kowanne ɓangare zasu shiga zuwa ɗaya yankin a mako.

Wannan ƙetara kan iyakar shine na farko tun shekara ta dubu da ɗari tara da arba’in da bakwai lokacin da ƙasashen na yankin Asiya suka shiga yaƙi na farko a cikin yaƙi biyu da ƙasashen suka yi sabili da yankin Himalayan. Watan jiya aka tsaida yarjejeniyar buɗe kan iyakar domin gudanar da harkokin cinikayya da juna.



A halin da ake ciki kuma, jami’an ƙasar Pakistan zasu gana da na asusun bada lamuni na duniya a Dubai yau, yayin da ƙasar dake yankin Asiya take fama da matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki. Masu kula da lamura sun ce Pakistan na bukatar kimanin dala miliyan dubu uku zuwa huɗu domin daidaita harkokin tattalin arzikinta da kuma gujewa gaza biyan basusukan ƙasashen ƙetare da ake binta, wanda bisa ga sharaɗi ya kamata ta kammala biya shekara mai zuwa.

Tsadar rayuwar ƙasar yana kimanin kashi 25% yayinda kuɗin ajiyarta suke dab da ƙarewa. Ƙasar wadda ta mallaki makaman nukiliya, kuma babbar abokiyar ƙawancen amurka a yaƙi da ta’addanci, tana fama da ruɗamin siyasa da gwagwarmaya da mayaƙan kishin islama dake kan iyakar Afghanistan da kuma matsalar kuɗi da ta shafi ƙasashen duniya. Jami’an harkokin tattalin arziki na ƙasar Pakistan sun ce zasu nemi agajin kuɗi na gaggawa daga asusun IMF ne kawai a matsayin matakin ƙarshe na shawo kan matsalar.

XS
SM
MD
LG