Hare-haren na bam da aka boye cikin mota sun kashe mutane akalla 8, wasu 20 suka ji rauni a yankuna uku cikin babban birnin, yayin da harin na kwanson bam ya kashe mutane hudu a gundumar Azamiyah.
Muqdadiyah dake arewa maso gabas da babban birnin wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin motar tanka ta mai da yake ciki a wani wurin binciken ababen hawa a kusa da wani sansanin sojan Iraqi, ya kashe kansa, ya raunata wasu sojoji 6.
Rundunar sojojin Amurka ta ce an kashe mata sojoji 4, ciki har da na kundumbala daya a fadan baya bayan nan a Iraqi. Jiya talata, ’yan gwagwarmaya sun kai hare-hare da dama cikin Iraqi suka kashe mutane fiye da hamsin, da yawa daga cikinsu kuwa ’yan mazhabin Shi’a dake ibadar rana mafi tsarki gare su ta Ashura.