Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinu Sun Koma Teburin Shawarwari A Birnin Kudus


An koma Teburin shawarwari tsakanin Isra’ila da Falaasdinu a birnin kudus,kuma duka sassan zasu fiskanci matsin lamba saboda sun gaza aiwatarda sharudda da kasa da kasa suka amince dasu cikin shirin wanzarda zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Babban Janar a runudnar mayakan Amurka, William Fraser, yana ganawa da Frime Ministan yankin Falasdinu Salam Fayyad,da Jami’i daga Ma’aikatar Tsaron Isra’ila Amos Gilad.Ministan Tsaron Isra’ila Ehud Barack, ya kauracewa taron,ya tura Gilad ya wakilceshi.

Shugaba Bush ya wakilta Janar Fraser ,ya sa ido kan ci gaba da ake samu a wajen aiwatarda taswirar wanzarda zaman lafiya da aka kaddamar a 2003. Wasu daga cikin abinda taswirar tayi tanadi akansu harda neman Isra’ila ta tsaida duk wani aikin gine ginen fadadawa a Yankin Kogin Jordan,ita kuma yankin Falasdinu ta shawo kan masu gwagwarmaya.

Babu sashe da ya aiwatarda nasa banagare.

XS
SM
MD
LG