Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Diplomasiyyar Amurka Zai Ziyarci Tibet


Wani jami’in Amurka, yana shirin sauka a Tibet a yau Juma’a, a daidai lokacin da irin wannan ziyara ta manema labarai ‘yan kasashen waje ta ci tura a jiya.

Jiya Alhamis a birnin Washington DC, Ma’aikatar harkokin Wajen Amurka tace an gaiyaci jami’in diplomasiyyar Amurka yaje domin a zagaya birnin Lhasa da shi. Lhasa dai shine babban birnin Tibet kuma a nan arangama tsakanin ‘yan sandan China da masu zanga zanga tafi tsanani.

Jami’in diplomasiyyar da ba a baiyana ko waye ba, zai kasance a Lhasa har zuwa gobe Asabar. A wata sabuwa, malaman addinin Bhudda sun gaya wa ‘yan jaridar dake ziyartarLhasa a halin yanzu, cewa China ta kantara karya, wajen baiyana wanda ke da laifin zanga zangar ta Tibet.

Malaman sun fashe da kuka a lokacin da suke gaya wa manema labaran cewa jami’an tsaron China sun tafka barnar rayuka da dukiyoyi a yankin nasu.

XS
SM
MD
LG