Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyya Mai Mulkin Japan Tana Zaben Sabon Prime Minister


‘Yan Jam’iyyar Liberal ta Japan, zasu yi zabensu na cikin gida yau Lahadi, domin zaben sabon shugaban Jam’iyyar, wanda zai maye gurbin Prime Minister Shinzo Abe, bayan ya aje aiki haka kwatsam.

Kuri’ar jin ra’ayin ‘yan jam’iyya ta nuna cewa tsohon Sakataren Majalisar Zartaswa ta Kasa, Yasuo Fakuda, wanda ke da goyon bayan yawancin bangarorin jam’iyyar, shine zai lashe zaben.

Fakuda mai shekaru 71, yana takara ne da tsohon Ministan harkokin Waje, Taro Aso. Duk wanda ya ci wannan zaben, shine zai kasance Prime Ministan Japan, saboda Jam’iyyar ta Liberal ita ce ke da rinjaye a majalisar kasar.

Za a zabi sabon Prime Ministan ne a wani zabe da za a gudanar a majalisar, ranar Talata. Shinzo Abe ya sauka daga mukaminsa ranar 12 ga watan Satumba, bayan yayi abin da bai ma kai shekara daya ba a ofis.

XS
SM
MD
LG