Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Ta Nutsar Da Jirgin 'Yan Fashin Jirage A Somalia


‣Rundunar mayaƙan ruwan Indiya ta ce ɗaya daga cikin jiragen ruwan yaƙinta ya nutsar da wani jirgin ruwan ’yan fashin jirage a dab da gaɓar Somaliya.

Jami’an soja sun ce jirgin ruwan yaƙin na Indiya mai suna ‘Tabar’ yayi arangama da babban jirgin ruwan ’yan fashi da wasu ƙananan jirage biyu dake binsa da maraicen jiya talata. Hukumomi sun ce jirgin yaƙin na Indiya yayi ta nanata kira ga jirgin ’yan fashin da ya tsaya don bincike. Jami’an soja suka ce ’yan fashi daga cikin babban jirgin sun buɗe wuta kan jirgin na Indiya, wanda ya maida martani ya nutsar da jirgin ’yan fashin.

Wannan lamarin ya faru a mashigin ruwan Aden, inda jami’an zirga zirgar jiragen ruwa suka ce ’yan fashi sun sace wasu jiragen jiya talata. Hukumomi suka ce ’yan fashi sun sace wani jirgin kamun kifi na ƙasar Thailand ɗauke da ma’aikata 16, da wani jirgin ɗaukan kaya na Iran mai ma’aikata 25 da kuma wani jirgin ruwan Girka mai ma’aikata aƙalla 23.

A halin da ake ciki, jami’an Amurka sun ce ’yan fashin da suka saci wani jirgin ruwan ɗaukar man fetur na Sa’udiyya da ma’aikatansa su 25 sun tafi da jirgin zuwa tashar jiragen ruwan Harardhere, wata tunga ta ’yan fashin jirage.

XS
SM
MD
LG