Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kamfanonin Duniya Sun Fadi,Ko Kuma Ribar Da Suke Samu Tayi Kasa,Wannan Ya Girgiza Kasuwannin Saida Hannayen Jari A Sassan Duniya.


Sakamakon rahotannin karancin riba ko faduwa daga manyan kamfanonin Duniya, wannan yana haddasa fargabar koma bayan tattalin arzikin Duniya,wadda ya girgiza kasuwannin saida hannayen jari a sassan Duniyar daban daban.

Kasuwar saida hannayen jarin Amurka ta bude hada hadar yau da faduwar hanu. Manyan kasuwannin saida hannayen jarin a Turai duk sun zube da kamar kashi uku zuwa sha biyun ranar yau. Haka ma kasuwannin saida hannayen Jari a Asiya duk sun yi kasa,ta Tokyo ta fadi da kusan kashi 7,yayinda kasuwar Hang Seng ta Hong Kong,da Kospi dake Seoul, sun fadi fiyeda kashi biyar cikin dari a karshen yinin yau.

Amma matsalar kudin bata tsaya kasuwannin saida hannayen jarin ba kurum,ta taba ma'aikata ako wani rukuni,har ta tilasta musu sake inda suke cin abinci. Maciyar Abinci ta McDonald,kantin cin abinci mafi girma a Duniya, ya bada labarin ribar da yake samu ta cira samakon karin masu zuwa wurin cin abinci saboda arha,musamman sashen abincin da bai dara dala daya ba.

XS
SM
MD
LG