Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa


Akwai alamun samun karin ambaliyar ruwa a kasashen yammaci da tsakiyar Africa, bayan anyi makonni ana maka ruwa kamar da bakin kwarya, wanda ya rusa gidaje, ya wanke gonaki, ya kashe dabbobi da daruruwan mutane.

Wata kakakin Ofishin Gudanar da Aiyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya, Elizabeth Byrs, tace wannan mamakon ruwa ya shafi a sama da mutum dubu dari biyar a kasashen Africa ta Yamma guda 12.

Kakakin Ofishin Aiyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniyar, kuma tace ruwan da ya kwankwanta a unguwannin jama’a, da yanayin zafi da ya biyo bayan ruwan, zai kara taimakawa yaduwar farin dango.

Tace kasashen mali da Jamhuriyar Nijar sune suka fi fuskantar wannan hadari, inda fari kan cinye amfanin gona, da ma ciyawar da dabbobi zasu ci, wanda kan haifar da matsalar yunwa.

Shima Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross, mai kula da Yammaci da Tsakiyar Africa, Alasan Sengore yace gwamnatocin Africa basu da wadatattun kudi ko kayan aikin da zasu iya tunkarar wannan bala’i, kuma su taimakawa wadanda abin ya shafa a kasashensu.

XS
SM
MD
LG