Hannayen
jari a kasuwannin zuba jari na duniya, sunyi faduwar da basu taba ganin irinta
ba a shekaru masu yawa, inda aka tafka asarar abin da ya kai dollar biliyan
dubu biyu a rana daya kawai.
An
fi samun faduwar jarukan a kasashen Turai, da kasashe masu tasowa. Dukkan
kasuwannin zuba jari guda goma sha takwas na kasashen turai sun zabgo kasa, .
Babbar kasuwar zuba jari ta London tayi rashin kashi tara bisa dari, faduwa
mafi girma da ta taba gani cikin kimanin shekaru ashirin. Kasuwannin Rasha
sunyi faduwar kashi 19 bisa dari.
Masu
hannayen jari sunyi ta rige-rigen sayar da jarukansu, bayan da manyan bankunan
kasashe duniya suka rika daukar matakan kare kudaden da mutane suka ajiye a
bankuna, domin a tabbatar da tsaron asusun su. Saida gwamnatocin Denmark da
Jamus suka dauki matakan shiga kai tsaye, domin ceto wasu bankuna da suka
tasamma rugujewa.
Ta
fuskar kudaden musaya kuwa, darajar Euro wanda akle amfani da shi a kasashen
Turai guda goma sha biyu, ta yiwo kasa da kashi shida bisa dari, a kan Yen na
Japan, faduwar da bai taba irinta ba.
Wata
masaniyar harkokin tattalin arziki, Sandy Batten ta banin Morgan Chase, tace a
hangenta, tattalin arzikin Amurka ya tasamma rugujewa.