Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Agaji Sun Fara Isa Burma


Gwamnatin Mulkin Sojin Burma, tace tana maraba da kayan agaji daga kasashen duniya, domin tallafawa wadanda guguwar Nargis ta yiwa ta’annati, amma bata bukatar wadansu ma’aikatan agaji.

Wata sanarwa da aka bayar daga Ma’aikatar Harkin Wajen Kasar, a jiya Juma’a, tace Burma zata yi amfani da ‘yan kasarta wajen rabon kayan agajin.

Sanarwar tace tuni ma har kasar tayi waje da wani jirgi, dauke da ma’aikatan ceto, tare da ‘yan jarida, wadanda suka shiga kasar ba tare da izini ba.

Gwamnatin Mulkin Sojin Kasar tana shan iza wutar sai ta kyale ma’aikatan agaji su shiga kasar, domin agazawa sama da mutum miliyan daya dake cikin halin kaka-nika yi.

Shugaban Hukumar Kula da Agaji ta majalisar Dinkin Duniya, John Holmes, yace an shiga wani mawuyacin hali a yanzu haka. A hain yanzu dai guguwar ta kashe a kalla mutum dubu 23, dubu 42 kuma sun bace.

XS
SM
MD
LG