Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ragargaji Manyan Kasashen Duniya


Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan manyan kasashen duniya da karyewar tattalin arziki kewa barazana, sun fara karya alkawurran da sukai na samar da abinci ga miliyoyin mayunwata a kasashe masu tasowa.

Mr. Annan yayi wannan jawabi ne a wani jawabi da ya gabatar wajen wani taron kasa da kasa kan yunwa, wanda aka gudanar a birnin Dublin.

Yace kimanin kananan yara dubu goma daga sassan duniya dabam-dabam ne zasu mutu a daidai lokacin da yake jawabi a jiya, sakamakon karancin abinci mai gina jiki.

Annan yace lallai ne a baiwa matsalar karancin abinci cikakkiyar kulawa, kamar yadda ake baiwa bankuna masu fuskantar karayar arziki.

Yace kasashen duniya masu arziki, tare da manyan kafofin bada rance, suna ta kashe billiyoyin daloli wajen tallafawa tattalin arzikin manyan kasashe, amma an bar matalautan duniya yunwa tana kashe su.

A sakon da ya aike wajen taron, Paparoma Benedict, ya dora alhakin halin da mayunwatan duniya ke ciki, kan yadda kasashen duniya masu arziki suka maida hankulansu kan tara abin duniya.

XS
SM
MD
LG