Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban A Pakistan Ta Dakatarda Shawarwari Da Gwamnati


Babban kwamandan mayakan Taliban a Pakistan ya dakatar da shawarwarin sulhu na ba-sabam ba da Gwamnatin kasar.

Kakakin Baitullah Mehsud ya fada yau litinin cewa, Mehsud ya dakatar da shawarwari da Gwamnatin ne saboda ta ki janye dakarun ta daga yankin Kabilu dake kan iyaka da Afghanistan. Zuwa yanzu dai Gwamnatin Pakistan bata tanka kan wannan mataki da Mehsud ya dauka ba.

Cikin makon jiya, Mehsud ya umurci mayakan sa su daina kaiwa sojojin Pakistan hari, bayan da rahotanni suka fito cewa Gwamantin Pakistan tana shawarwari kan matakai 15 na cimma zaman lafiya da ‘yan kungiyar.Mehsud ne babban kwamandan kungiyar ‘yan gwagwarmaya mai suna Tehrik el Taliban mai zama a yankin Waziristan.

Amurka da shugaban Pakistan Pervez Musharraf suna zargin Mehsud da laifin tsarawa da aiwatar da kisan tsohuwar PM Benazir Bhutto a bara, Zargin da Mehsud ya musan ta.

XS
SM
MD
LG