Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Yaki Da Rashawa A Najeriya Tace A Binciki Obasanjo


Wata kungiyar yaki da rashawa da cin hanci a najeriya, ta bukaci ayi cikakken bincike kan barnar da aka tafka a zamanin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo. Shugabannin Gamayyar Kungyoyin Yaki Da Azzaluman Shugabanni, sun bada wata sanrwa dake cewa lallai ne a kafa wani kwamitin bincike, domin a dawo da martabar gwamnati a idon talakawan kasa.

Shugaba Obasanjo dai yana shan suka kan yadda ya barnatar da biliyoyin naira kan aiyukan da suka gaza inganta rayuwar talakawa. Shugaba Umaru Musa ‘Yar Aduwa yace ba zai lamunci rashawa da cin hanci a sabuwar gwamnatinsa ba, amma kuma wasu suna ganin da kyar in zai iya tabuka wani abu kan Obasanjo, tunda shine ya tsamo shi, ya tsaida shi takarar Shugabancin kasar.

Shekaranjiya talata Ministar Lafiya da mataimakinta suka rasa mukamansu sakamakon gararuma da aka cve sunyi ta kimanin dollar Amurka miliyan uku, wato kusan naira miliyan dari hudu.

Saidai wani dan jam’iyyar adawa ta ActionCongress, Mr. Lai Mohammed yace tilas ne gwamnatin ‘yar Aduwa ta nuna da gaske take yi.

XS
SM
MD
LG