Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyi A Jos Sun Soki Lamirin Tsige Gwamna Dariye


Kungiyar Lauyoyi a Nigeria ta yi allawadai da hanyoyin da aka bi, wajen tsige gwamna Joshua Chibi Dariye na Jihar Filaton Najeriya. Tayi bayani da kakausar Murya a wata sanarwa da ta bayar a Jos, ranar Talata cewar, wannan hali ya saba wa kundin tsarin mulkin Nigeria.

Babban Sakataren Kungiyar Lauyoyin ta Nigeria, Lawal Rabana ya ce ganin kasancewar ’yan majalisa shida ne kacal daga cikin ashirin da hudu suka zartas da hukuncin tsigewar, ya nuna cewa hakika tsigewar ba ta cancanta ba ko kadan.

Rabana ya ce mu a gare mu, wannan keta tanade tanaden tsarin mulkin kasa ne. Tsarin Mulkin Najeriya dai, lallai sai kashi biyu bisa uku na ilahirin ‘yan majalisar sun amince, kafin a zartar da tsigewar.

Saboda haka, inji Rabana, “mu a gare mu wannan tsigewar ba ta dace ba kuma ba ta samu karbuwa ba.” Ya zuwa yanzu dai, gwamnonin jahohi biyar aka tsige daga mukamansu, a wani yanayi da ke nuni da irin dabarun kam- karya da barazana, da gwamnatin shugaba Obasanjo ke amfani da su wajen gudanar da mulkin danniya a kasar.

Dama dai ana ta zargin Shugaba Obasanjo da fito da wadansu halaye dake nuna cewa ba da gaske yake yi ba, wajen shirin gudanar da zabe watan Afrilun shekara mai zuwa, amma dai ya sha musanta zargin.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa, wacce kuma ake zargin tana yiwa gwamnonin da basa tare da shirin Obasanjo na tazarce bita da kulli, inda ta lashi takobin kawar dasu daga kan mulki ko da ha-maza ha-mata, domin ta sami sukunin musguna masu, tunda tsigesu daga kan mukamansu, zai yaye masu kariyar da suke da ita.

Shidai mai magana da yawun hukumar ta EFCC Osita Nwajah bai boye murnarsa ba da rawar da ’yan majalisssun Jihar Filato su shida suka taka wajen tsige Gwamna Dariye, ko da kuwa yana bisa ka’ida ko a’a.

Nwaja yace ya kamata mutane su jinjina wa ‘yan majalisun, ba su rika yi masu alla- wadai ba, domin sunyi abin daya dace.

Yace hukumarsa ta EFCC tana murna matuka, tana kuma alfahari wadannan mambobin majalisar na jihar Plateau, wadanda suka yi abinda ya dace.

Masu nazarin al’amuran yau da kullum suna ganin tsige tsigen na iya kasancewa wani al’amari mai tada hankali da kuma zai iya kawo sanadin kazamin rikici a wannan kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika, wanda zai iya baiwa Shugaba Obasanjo hujjar kafa dokar ta baci ya kuma cimma burisa na tazarce.

XS
SM
MD
LG