Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Ta Bada Wa'adin Janye Sojin Amurka Daga Iraq


Majalisar ta kada kuri’ar amincewa da kudurin a jiya Alhamis, da rinjayen kuri’au 22, inda masu so suka sami kuri’u 223, masu adawa da kudurin kuma suka sami 201.

Kudurin ya bukaci shugaba Bush da ya sanar da majalisar idan ana bukatar karin wa’adin zaman sojojin don wadansu bukatu da ba na yaki ba, kamar horas da sojojin Iraqi, da kuma kare jakadun kasashen waje.

Gwamnatin Shugaba Bush ta gabatar da rahoton irin ci gaban da aka samu a Iraq a jiya Lahadin, inda tace nasarar da kaka samu ta fuskar siyasa da aikin soja, bata taka kara ta karya ba.

Amma Shugaba Bush ya nace kan cewa har yanzu za a iya saimun nasara, ya kuma bukaci Majalisar da sauran jama’ar kasa, da kada suyi saurin yanke hukunci har sai nan da ‘yan watanni masu zuwa.

Rahoton ya nuna cewa an sami nasarori a fannoni takwas daga cikin goma syha takwas da aka zaiyana.

XS
SM
MD
LG