Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Ministocin Najeriya Ta Ce Shugaba Yaradua Yana Karfin Ci Gaba Da Gudanarda Aikinsa Duk Tafiyar Neman Jinya


Majalisarzartaswar Najeriya ta yanke hukunci cewa shugaba Umaru Musa ‘Yaradua yana da karfin ci gaba da aikinsa duk da wata biyu da ya yi baya kasar.Matsayar majalisar ta saba da ta majalisar dattijai, wacce tace tilas shugaban kasa ya sanarda majalisar dokoki cewa zai yi balaguro,matakida zai mika iko ga mataimakinsa.

Jiya Lalata aka tsaida shawarwarin duka biyu,lokacinda jami’an gwamnati suka yi muhawara kan ko shugaba ‘Yaradua yana iya ci gaba da tafiyarda aikin sa. Ya bar Najeriya a karshen watan Nuwamba zuwa Saudiyya domin neman jinya na larurin zuciya. Haka kuma shugaban yana fama cutar koda.

Majalisar zartawar ta tsaida wan nan shawarar ce ,kasa da mako daya, bayan wata kotu ta ba ta wa’adin mako biyu ta tsaida shawarar ko shugaba ‘Yar’adua yana da karfin ci gaba da gudanarda aikinsa.

Ahalin yanzu kuma,shugabannin kugiyoyin addini da masu kare hakkin bil’adama sunce sakonnin Text da aka aike ta woyoyin Celula sun taimaka wajen ruruta wutar rikici data halaka mutane da dukiyoyi a Jos.

Shugaban daya daga cikin kungiyoyin farar hula masu zaman kansu, Shehu Sani yace kungiyarsa ta tattara bayanai sakonnin Text 150, da aka yi ta aikawa lokacinda rikicin yake ci. Shehu Sani ya fada jiya laraba cewa,wasu sakonnin sunacewa “Ku yanka su kamin su yanka ku” ku wurgasu cikin rami kamin su wurgaku".

Masu rajin kare hakkin bil’adama dana addinai, sunce sakonnin an auna su kan kiristoci da ma musulmi.

XS
SM
MD
LG