Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malawi Ta Karbi Shugabancin Tarayyar Afirka Bayan Yunkurin Qaddafi Na Neman Tazarce Ya Faskara


Kasar Malawi ta karbi shugabancin tarayyar Afirka,bayan zazzafawar muhawara a majalisar zartaswar kungiyar.Shugaban kasar Malawi Bingu wa Murtharika, zai zama shugaban kungiyar na shekara mai zuwa.

Shugaban Libya Moammar Gaddafi, ya yi kamfen na neman wa’adi na biyu a shugabncin kungiyar na shekara shekara,domin kara yakin neman hade nahaiyar ta zama kasa karkashin hukuma daya,shigen na Tarayyar Turai. Amma shugabannin Afirka suka ki amincewa da bukatarsa jiya lahadi a Addis Ababa fadar kasar habasha.

Bayan ya kasa samun biyan bukata,Mr.Kaddafai ya yi suka ga takwarorinsa cewa ragaye ne a fagen siyasa. Ya soki lamirin kungiyar mai kasashe 53 da cewa suna bata lokaci wajen yin jawabai masu tsaho,da zartas da kudorori,alokaci guda kuma suna kauda kai daga sauran Duniya dake sakewa. Duk dahaka,yace zai ci gaba yakin neman hada kan nahiyar.

XS
SM
MD
LG