Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

McCain da Obama Sun Tsananta Yakin Neman Zabe


Da kamar kwannaki 10 kafin zaben shugaban kasan da za’ayi a Amurka, jiya ‘yan takaran biyu – Barrack Obama na Democrats da John McCain na Republicans, sun wuni suna ta kyamfen ne a jihohin yammacin Amurkar, wadanda ake ganin muhimmai ne ga duk wanda ke son shiga fadar White House.

Wani sabon binciken jin ra’ayin jama’a da cibiyar bincike ta Real Clear Politics ta gudanar ya nuna cewayanzu ratar da Obama ya baiwa McCain a tagomashin jama’a ta kai ta maki 8.

A jawabin da yawa magoya bayansa jiyan a jihar New Mexico, Mr. McCain ya ja kunnensu da su san cewa muddin suka zabi Obama, kamar kuma sun mika majalisar dokoki da ita fadar ta White House na ga hannun ‘yan Democrats.

Ya sake nanata cewa Obama zai dirka musu haraji mai yawan da zai wahalarda masu matsakaicin karfi da kuma kananan “yankasuwa na Amurka.

Shi kuma da yake tasa laccar a jihar Nevada a jiyan, Barack Obama ya sake tunatarda mutane cewa ba fa wani banbanci tsakanin manufofin tattalin arziki na John Mccain da shugaban Amurka na yanzu George Bush, har ya kuma tunatarda su cewa Bush ya ma riga yaje ya jefawa McCain kuri’arsa.

Binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna cewa maganar tabarbarewar tattalin arzikin nan dai na cikin abubuwan da suka taimakawa Obama tserewa McCain a wannan takarar.

XS
SM
MD
LG