Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Amurka Mai Barin Gado George Bush,da Magajinsa Barack Obama, Sun Gana A Fadar White House Jiya Litinin


Jami’an fadar White House sun ce shugaba George Bush da shugaban ƙasa mai-jiran gado Barak Obama sun yi zama mai amfani cikin yanayin jin daɗi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da sabon shugaban ƙasar zai fuskanta idan ya hau karagar mulki.

Mr. Bush da Mr. Obama sun gana jiya Litinin karo na farko tunda Mr. Obama ya lashe zaɓen shugaban ƙasa. Sun yi tafiya tare a harabar Fadar shugaban ƙasa ta White House daga baya zuka yi wani zama a kaɗaice a ofishin shugaban ƙasa dake fadar mulkin.

Kamfen na Mr. Obama ya bada sanarwa inda ya bayyana gamsuwa da yadda shugaba Bush ya nuna sha’awar ganin an miƙa mulki lami lafiya. Wata majiya da ta san yadda zaman na jiya ya kasance ta ce Mr. Obama ya yi kira ga shugaba Bush ya da ya goyi bayan bada rance na gaggawa ga masa’antun ababan hawa da ke neman durƙushewa.

Shugaban ƙasar mai jiran gado ya kuma nemi Mr. Bush ya gabatar da bukatar bada wani sassauci ga ma’aikata a zaman ƙarshe da za a yi da majalisa mai ci yanzu. Yayinda Mr. Bush da magajinsa suke ganawa, mai ɗakinsa Laura Bush kuma ta zaga da mai ɗakin shugaban ƙasa mai jiran gado Michelle Obama domin nuna mata kowane saƙo a fadar shugaban ƙasar.

XS
SM
MD
LG