Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mugabe shugaban Jam’iya mai mulki a Zimbabwe ta zargi shugaban jam’iyar adawa Morgan Tsvangirai da hana ruwa gudu


Jam’iya mai mulki a Zimbabwe ta zargi shugaban jam’iyar adawa Morgan Tsvangirai da hana ruwa gudu a shirin aiwatar da yarjejeniyar raba madafun iko, bayan da Tsvangirai ya ƙi halartar taron ƙolin yankin da aka kira domin ceto yarjejeniyar.

Kafofin watsa labarai sun ambaci ta bakin babban jami’in shiga tsakani na jam’iyar ZANU-PF da cewa da alama Tsvangirai yana ɗari ɗarin ganin an cimma matsaya a tattaunawar kafa ɗaunin iko. Shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe da wasu shugabannin shiyar da dama ne suka taru a birnin Swaziland domin halartar taron ƙolin da jiya Litinin.

Sai dai Tsvangirai bai halarci taron ba da hujjar cewa gwamnati taƙi sabunta passpo ɗinsa. Jam’iyar MDC tace ƙin sabunta passpo ɗin na Tsvangirai raini ne, kuma alama ce da ta nuna cewa, ZANU-PF bata da niyyar raba madafun iko.

An ɗaga zaman tattaunawar zuwa Litinin mai zuwa a Harare. Tattaunawa tsakanin jam’iyar ZANU-PF da MDC ta cije ne sabili da kasa cimma matsaya kan jam’iyar da zata jagoranci waɗansu manyan ma’aikatu.

XS
SM
MD
LG