Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitaccen Masani Kan Tattalin Arziki,Dan Amerika Krugman,Ya Sami Lambar Yabo Ta Nobel


Fitaccen masanin kimiyyar tattalin arzikin nan na Amurka Paul Krugman ya sami nasarar samun lambar yabo ta Nobel ta wannan shekarar 2008 kan kimiyyar tattalin arziki.

Litinin din nan cibiyar nazarin kimiyyar tattalin arziki ta Sweden ta bada sanarwar baiwa Farfesa Krugman lambar yabo,saboda gano wata sabuwar hanyar bunƙasa tasirin tattalin arzikin birane a ƙasa da ƙasa.

Krugman, shehin Malami ne dake koyarwa a jami‘ar Princeton New Jersy, kuma marubuci ne na maƙalolin cinikayya a jaridar The New York Times. Kuɗin da aka shirya bashi zai kai Dola miliyan ɗaya da dubu ɗari shida.

XS
SM
MD
LG