Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Jiran Gado,Barack Obama,Ya Yi Taronsa Farko Da Manema Labaru Tun Bayan Samun Nasara Zabensa


Shugaban Amurka Mai Jiran gado Barack Obama a yau Jumma'a yayi jawabinsa na farko ga taron manema labarai inda ya bayyana matakan da Gwamnatainsa ke shirin dauka domin farfado da tattalin arzikin Amurka.

Barack Obama yace zai kokarta daukan muhimman matakai domin saukaka tsarin daukan bashi da biyan bashin, da yanzu ke addabar Bankunan da kananan 'yan kasuwar Amurka, ya kuma yi alkawarin daukan matakan karfafa gwiwar kananan ma'aikata musamman masu iyali. Shugaban mai jiran gado Barack Obama, ya nbulla a wajen tattaunawar da manema labarai tareda tawagar jami'an da ya nada domin yin gyaran fuska ga tattalin azrikin Amurka domin ya koma kan turba.

Tuni daman Barack Obama, ya nada babban jami'in lura da muhimman ayyukan fadar shugaban kasa, Rahm Emmanuel, kuma dan Majalisar wakilan Amurka daga mazabar Illinois. Kafin hira da manema labarai saida ya gana da masu bashi shawara kan harkokin tattalin arziki a birnin Chicago, dake tsakiya maso yammacin Amurka. Cikin wadanda ke cikin wannan kwamiti na masu bashi shawara harda manyan kusoshin Gwamnati a yanzu da na da,da kuma manyan kusoshin 'yan kasuwa,kamar mashahurin dan kasuwan nan, Warren Buffett. Har wa yau masu halartar wannan taro sun hada da tsohon Sakataren Baitul Malin Amurka, Lawrance Summers,da kuma tsohon shugaban babban Bankin Amurka, Paul Volcker. Dukkansu biyu an ambaci sunayensu cikin wadanda za a nada sakataren Baitul Mali.

Shugaban mai jiran gado ya kuma bayyana cewar zai bada amsa ga wasikar taya murnar da shugaba Amadineejad na Iran ya aiko masa bayan bayyana sakamakon zabensa da ya sami nasara.

XS
SM
MD
LG