Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton Tace Barazanar Masu Matsanancin Raayin Islama Kan Amurka Ta Fi Ta Shirin Nukiliyar Iran Da Koriya Ta Arewa


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace kungiyoyin masu matsanancin ra’ayi da suka ratsa kasa da kassa,masu da’awar Islama, sun fi barazana ga Amurka fiyeda shirin Nukiliyar Iran da KTA.

Clinton tace gwamnatin Obama ta damu gameda kungiyoyin da ba kasashe ne ba da suke da alaka da al-Qaida,wadanda suke da sansanoni a Afghanistan,Pakistan,Saudiyya,Yemen da kuma a yammacin Afirka.

Clinton ta fadi hakane cikin hira datayi da tashar talabijin ta CNN da aka nuna jiya lahadi. Tace babu shakka shirin Nukiliyar Iran da Koriya Ta Arewa barazana ce ta hakika. Farisa ta musanta zargin tana kokarin kera makaman Nukiliya,tana mai cewa shirin ta na zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG