Ministan kuɗin Nigeria Shamsudeen Usman yace faɗuwar da farashin mai keyi a kasuwa yasa ala tilas a rage yawan kuɗin da za’a kashe a kasafin kuɗin shekara mai zuwa.
Dr. Shamsudeen Usman yau Juma’a a birnin Tarayya na Abuja yake shaidawa manema labarai cewa bashi da zaɓin da ya wuce rage kuɗin kasafin a kowane ɓangaren da Gwamnatin ke gudanar daayyukanta. Daman dai tattalin arzikin Nigeria ya ta‘allaka ne a kan man da atake saidawa ƙasar waje, domin a kan farashin ne Nigeria ake tsara kasafinta kowace shekara.
A halin da ake ciki, Ma’aikatar lafiyar
Nigeria ta bada sanarwar samun nasarar daƙile bazuwar ciwon amai da
gudawa-Cholera- sanarwar ma’aikatar tace jihohi biyar sun tagaiyara
sosai kafin cin ɗungumin cutar. Babban Darekta a ma‘aikatar lafiya Dr.
Abdul Nasidi yayi ƙarin haske kan matakan da aka ɗauka kafin a kai ga
samun nasarar. Dr. Nasidi
yace haƙiƙa jami‘an lafiya sun tabbatar da ɓullar cutar Cholera a wasu
majalisun kananan Hukumomi.