Shugaban Amurka George Bush yana ci gaba da ziyararsa zuwa kasashen Latino, inda ranar Asabar ya zanta da shugaban kasar Uruguay, Tabare Vazque a garin Colonia. Shugaban na Uruguay yana fatan Amurka zata bude kofar ta don ‘yan kasuwar kasarsa su iya kawo hajojinsu, su saida.
Sai dai a jiya ma dubban masu zanga-zanga sun cika titunan Montevideo, babban birnin na Uruguay a ci gaba da zanga-zangar nunawa shugaba Bush kyama.
Kuma shugaban Venezuela, Hugo Chavez shima ya bar kasarsa yayi tataki har zuwa cikin Argentina don jagorancin dubun dubatar masu irin wannan zanga-zangar nuna tsanar shugaba Bush.
Bush din dai yace “ba a yiwa Amurka adalci” a kan wadannan al’amura, saboda ba a kulawa da kokarin da take yi na inganta rayukkan mutanen yankin.