Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soja Sun Tunkude Gwamnatin Kasar Fiji


Bayan makonni suna kurari, a karshe dai sojojin Fiji sun aiwatar da barazanar da sukayi. Babban Hafsan Hafsoshin kasar Commodore Frank Bainimarama ya karbi ragamar mulki bayan ya rusa gwamnatin dimokradiyya.

Yace ya dauki wannan mataki ne saboda abinda ya kira “Uwar wuya” ko kuma tilas da tasa ya dauki wannan mataki saboda kasar ta doshi rushewa, karkashin jagorancin Firayim Minista Laisenia Qarase.

Kwamandan mayakan saman ya gayawa manema labaru cewa cin hanci da rashawa sunyi kanta a tsakanin jami’an gwamnatin kasar, kuma gwamnatin bata da niyyar warware matsalolin siyasar Fiji.

“Mun san cewa Fiji ta shiga wani hali,kuma gwamnati da dukkan wadanda aka dankawa amana karkashin tsarin mulkin demokradiyyar mu,sun gaza tsaida shawarar da zata kare al’umarmu daga kaiwa ga hallaka.”

Inji Kwamandan. Rundunar sojan kasar suna gardama da Firayim Minista Qarase kan shirinsa na yin afuwa ga wadanda suka shirya tawaye a kasar, shekaru shida da suka wuce.

Sojojin suna ganin an yiwa wadanda suka shirya juyin mulkin na baya sassauci ainun. Akwai kuma wata takaddamar kan wani shiri da zai bada fifiko wajen rabon filaye ga yan kasar na asali, wadda hakan zai basu fififko kan tsirarun kasar ‘yan kabliar Indiyawa.

Bainimarama wanda yake ganin kansa a matsayin garkuwa ga dukkan jama’a da al’adun Fiji, ya soki gwamnatin Qarase da danne hakkin tsirarun kasar, Indiyawa marasa rinjaye,wadanda yawansu kashi 40 ne cikin dari na al’umar kasar.

Sojojin zasu nada Firayim Minista na wucin gadi, daga bisani kuma a kafa gwamnatin riko. Commodore Bainimarama yayi alkawarin za’ayi zabe. Ya bukaci al’umar kasar da kada suyi fargaba ko tsoron matakin da ya dauka.

Firayim Minista Qarase da aka hambare yanzu anyi masa daurin talala cikin gidansa. Daga chan ne ya zargi sojojin da yiwa tsarin mulkin kasar hawan kawara.

Ya bukaci taimakon soja daga New Zealand da Australia domin wargaza juyin mulkin, amma duk kasashen biyu sunki,domin gudun jawo zub da jini. Babu shakka wannan juyin mulkin zai jawo suka daga kasashen duniya.

New Zealand da Australia sunyi gargadin cewa Fiji zata fuskanci mummunan tarnaki na tattalin arziki, muddin soja suka karbi ikon kasar. Wannan juyin mulkin shine na hudu a shekaru ashirin a Fiji, wata ‘yar karamar kasa dake kudancin Pacific.

XS
SM
MD
LG