’Yan sandan Indiya su na kyautata zaton cewa ’yan ta’adda ne suka kai wasu hare-hare da maraicen yau larabar nan a birnin Mumbai a kudancin kasar.
Kafofin labarai a birnin sun ce mahara dauke da manyan bindigogi da gurneti sun kai farmaki a kan wasu wurare hudu, ciki har da hotel-hotel biyu da tasoshi biyu na jiragen kasa, inda suka kashe mutane da dama.
’Yan sanda sun ce a yanzu haka, maharan sun killace kansu a daya daga cikin hotel-hotel din.