Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Sanata Barack Obama


An haifi Barack Obama, barbarar yanyawa tsakanin mutumin Kenya da ba’amurkiya ‘yar jihar Kansas, a shekarar 1961. Yayi wani bangare na kuruciyarsa a kasar Indonesia, daga baya kuma ya halarci Jami’ar Columbia da Kolejin Shari’a ta Jami’ar Havard duk a nan Amurka.

Aikin da Obama yayi na jami’in tsara aikin gayya, a Chicago, ya taimaka wajen kaifafa basirarsa ta hulda da jama’a, inda daga baya ya shiga siyasa, har yaci zaben shiga Majalisar Illinois.

A shekara ta 2004, an zabi Obama zuwa Majalisar Dattawan Amurka, dama kuma a wannan shekarar ce kwarjininsa ya bunkasa, lokacin da yayi wani jawabi a babban taron jam’iyyarsu ta Democrats.

Wannan jawabi mai tarihi, shine ya daga kimar Obama a siyasar Amurka, har yau gashi yana rike da ragama takarar Shugabancin Amurka na Jam’iyyarsa.

Yana da baiwar iya magana, kuma a fahimce shi, ga iya tsuma tarin jama’a da bakinsa. Kuzarinsa da kurucuyarsa suna taimaka masa kwarai. Wannan ya zo daidai da zamanin John F. Kennedy a shekarun 1960. Wannan ya bashi dama.

Saidai kuruciyarsa taso ta zame masa matsala, lokacin da abokan hamayya suka rika amfani da ita wajen nuna cewa bai shirya zama shugaban kasa ba. Hatta Hilary Clinton, babbar abokiyar hamayyarsa a zabukan fid da gwani, ta taba dago wannan magana.

Kamar yawancin ‘yan uwansa ‘yan Democrat, Obama yayi adawa da yakin Iraq, a yanzu kuma yana goyon bayan a tsaida ranar janye dakarun Amurka. Ya taba yin wani jawabi, inda yace.

Babu wata mafita ta soja a Iraq. Ba a taba samu ba. Babbar hanyar kare tsaronmu a Iraq, tare da tilastawa hukumomin kasar su warware matsalolinsu na cikin gida, ita ce mu fara janye dakarun mu. Ba nan da wata shida ko shekjara daya ba, yanzu.”

Masana sunyi ittifakin cewa Obama shine dan takarar shugabancin kasa, Bakar fatar Amurka mafi karfin goyon baya da aka taba yi a tarihin Amurka. Ana sa ran zai shawo kan dari-darin da fararen fatar Amurka keyi wajen marawa bakar fata baya.”

Wadansu har yanzu suna da tsoron cewa Bakar fatar Amurka zai iya samun matsalar cin zabe a Amurka. Ina ganin har yanzu akwai irin wannan matsala, amma Amurka fa ta ci gaba sosai a ‘yan shekarun nan, kuma kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya-bayan nan, ta nuna cewa Amurkawa zasu iya zabar baki ya kasance shugaban kasarsu.

Kasancewar Obama barbarar yanyawa, tare da baiwarsa ta iya jan ra’ayin jama’a, ta sanya shi a wani muhimmin matsayi a tarihin takarar shugabancin Amurka. Ranar hudu ga watan Nuwamba Amurkawa zasu nuna ko Amurkawa zasu dauki wannan mataki na tarihi?

XS
SM
MD
LG