Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Amurkawa Ke Zaben Sabon Shugaban Kasa


Amurkawa suna kada kuri'unsu a yau, domin zaben Shugaban kasa, bayan yakin neman zaben da aka ce ya fi ko wanne tsawo, ya kuma fi cin kudi a tarihin Amurka. Dan takarar Democrat Barrack Obama, yayi jawabin karshe a Jihar Virginia, a daren jiya, inda ya fuskanci dubun dubatar magoya baya.

A halin yanzu dai Obama shine ke kan gaba da a kalla maki bakwai a kuri'un jin ra'ayin jama'a, saida har yanzu ana iya cewa ba a san maci yuwo ba sai miya ta kare, musamman a wadansu jihohi masu muhimmanci da 'yan takarar ke hankoron kamewa.

Ba yawan kuri'un da mutum ya samu a babban zaben ne kadai zasu kaishi ga kujerar shugabancin kasar ba, a'a sai ma ya lashe a kalla kujeru 270 na Majalisar Dattawa tukuna.

Ba dai yawan kuri’un da mutum ya samu ne zasu kaishi ga dare kujerar shugaban kasa kai tsaye ba, a’a, yawan kujerun da jam’iyyar mutum ta samu a majalisar dattawa, ita ce zata kaishi ga wannan matsayi.

Dan takarar Republican Sanata John McCain na jihar Arizona, ya ziyarci jihohi bakwai ciki har da Florida, inda ya shaida wa magoya bayansa cewa shine zai lashe wannan zabe.

Suma ‘Yan takarar Mataimakan Shugaban Kasa, sun bazama neman kuri’u. Mai marawa Sanata McCain baya, Gwamnar Jihar Alaska Sarah Palin ta ziyarci jihohi biyar, ciki har da Iowa.

Shi kuwa dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na Jam’iyyar Democrat, Sanata Joe Biden na Jihar New Jersey, jihar da aka sani a matsayin ‘yar a bi yarima a sha kida, domin tarihin zabenta na shekaru hamsin, ya nuna cewa jam’iyya mai gwamnati suke zabe.

Ko ma meye sakamakon zaben na yau, zai yana da muhimmanci a tarihi. Idan Obama yayi nasara zai kasance bakar fata na farko da zai zama shugaban kasar Amurka a tarihi. Idan McCain mai shekaru 72 yaci, zai kasance mafi tsufa da zai zama shugaban kasa a tarihi. Mataimakiyarsa kuma zata kasance mace ta farko da za a zaba Mataimakiyar Shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG