Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Alhamis Zinedine Zidane Zai San Hukumcin Da FIFA Zata Yanke Masa


Shahararren dan kwallon kafar Faransa, Zinedine Zidane, yana dab da sanin irin hukumcin da za a yanke masa dangane da bugun da ya kai ma wani dan wasan kasar Italiya da kai a wasan karshe na cin kofin kwallon kafar duniya a Jamus.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta ce zata bayyana hukumcinta kan wannan batu a bayan taron sirri da zata yi yau alhamis a birnin Zurich a kasar Switzerland. Zidane zai bayyana a gaban wannan hukuma da zata zauna yau.

An fitar da zakaran dan wasan na Faransa daga wasan karshe a bayan da ya kayar da dan wasan Italiya mai suna Marco Materazzi a sanadin bugun da ya kai masa da ka a kirji a bayan musanyar miyawu tsakaninsu.

Zidane yayi ritaya a bayan wasan na ranar 9 ga watan Yuli a Berlin, wanda Italiya ta lashe a bugun fenariti. Zidane, wanda sau uku ana zabensa a zaman dan wasan kwallon kafa mafi shahara a duniya cikin shekara, yana iya fuskantar tara da kuma haramcin wasan da ba zai yi wani tasiri ba (tun da ya bar buga tamaula). Har ila yau ana iya kwace Kwallon Zinare da aka ba shi a matsayin dam wasan da ya fi burgewa lokacin gasar cin kofin duniya.

Shi ma Materazzi, wanda ya bayyana a gaban hukumar binciken da FIFA ta kafa a makon jiya, yana iya fuskantar tara da kuma haramta masa buga wasa.

XS
SM
MD
LG