Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Afghanistan an saki wani tsohon gwamna da aka sace makonni biyu da suka wuce


Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani

A Afghanistan an saki wani tsohon gwamnan Lardin kasar cikin koshin lafiya, bayan da wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka yi garkuwa da shi, a ranar 12 ga watan Fabrairu a Pakistan.

Fazulla Wahidi, wanda tsohon gwamnan Lardin Herat ne, ya gayawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an ceci shi ne a wajen wani shingen binciken ‘yan sanda da ke arewa maso yammacin Pakistan a birnin Peshawar.

Ya kara da cewa an yi ta musayar harbe-harbe bayan da aka ceto shi, kuma ya kara da cewa bai san wadanda suka yi garkuwan da shi a Islamabad ba makwanni biyu da suka gabata.

‘Yan sandan Pakistan sun gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa suna tsare da wasu mutane uku da ake zargi na da hanu a garkuwar da aka yi da tsohon gwamnan Lardin na Herat.

XS
SM
MD
LG