Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka gobe wasu jihohi zasu yi zaben fidda gwani na jam'iyyun Democrats da Republican


'yan takara a karkashin jam'iyyar Democrats
'yan takara a karkashin jam'iyyar Democrats

Masu zaben fidda gwani a karkashin jam’iyyar Democrat da Repblican, za su kada kuri’unsu a muhimmin zaben da za a yi gobe a juhohi biyar a nan Amurka.

Wannan zabe shi zai nuna wanda kowa ne dan takara jam’iyyun za su fitar.

Bayan zaben na gobe Talata, ana sa ran fiye da juhohin Amurka 50 za su fitar dan takararsu, yayin da ‘yan takarar da ke baya-baya wajen kokarinsu na kamo abokanan hamayyarsu da ke gaba-gaba a jam’iyyun biyu wato Donald Trump da Hillary Clinton.

Wani lokaci kuma da za a kuma damar samun dumbin wakilai a zbukan share fagen zaben gama garin da za a yi shine na ranar bakwai ga watan Yuni, a lokacin da masu fashin baki su ke ganin ‘yan takara da ke baya-bayan sun Makara.

Yanzu haka Trumo na da wakilai 460, Ted Cruz na da 370, Marco Rubio na da 163 John Kasich kuwa na da 63.

A bangaren ‘yan Democrat kuwa, Clinton na da wakilai 1,231, yayin da abokin hamayyarta Bernie Sander ke da 576.

Clinton ya zuwa yanzu ta samu samu fiye da rabin adadin wakilan da a ke bukata wato 2,383.

A bangaren Republican kuwa ana bukatar dan takara ya samu wakilai 1,237.

'Yan takara a karkashin jam'iyyar Republican
'Yan takara a karkashin jam'iyyar Republican

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG